'Yan gwagwarmaya a Iraqi na tinkarar Bagadaza

'yan gwagwarmaya na Islama a Iraqi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'yan gwagwarmaya na Islama a Iraqi

'Yan gwagwarmaya 'yan kishin Islama suna cigaba da kara dannawa suna tinkarar Bagadaza babban birnin Iraqi, to amma rahotannin baya-bayan nan sun ce akwai alamun sun samu tsaiko.

Wani wakilin BBC ya ce 'yan tawayen wadanda ke tafiya tamkar guguwa da rana, sun kwaci garuruwa - daga cikinsu kamar Tikrit, mahaifar Saddam Hussein mutane sun mika wuya ba tare da wani zubar da jini ba.

A garin Samara ne aka taka mu su birki, garin da nisan shi da Bagadaza bai wuce tafiyar sa'a 2 ba, kodayake wani wakilinmu yace lokaci bai rigaya ya yi ba da za a ce, karfinsu ya ragu a dannawar da suke yi kudancin kasar.

A ranar litinin ne suka fara kai harin lokacinda mayaka masu alaka da kungiyar al-Qaeda suka kwaci garin Mosul dake arewacin kasar.

Karin bayani