Ana taro kan Boko Haram a London

Sakataren harkokin wajen Birtaniya William Hague Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sakataren harkokin wajen Birtaniya William Hague

Ministocin harkokin wajen Nijeriya da kasashe makwabta na halartar wani taro a birnin London don tattaunawa kan matsalar Boko Haram.

Taron wanda sakataren harkokin wajen Britaniya William Hague ke karbar bakuncinsa, dori ne a kan taron kolin da aka gudanar a birnin Paris kan harkar tsaro a arewacin Najeriya a cikin watan jiya.

A yayin taron na London da za a ayi a gefen taron kolin na duniya kan kawo karshen cin zarafin mata, ministan harkokin wajen Najeriya Aminu Wali zai hadu da takwarorinsa na kasashen Benin da Chadi da Kamaru da Nijar.

Kana za su hadu da wakilan kasashen Birtaniya da Amurka da Faransa da Canada da Tarayyar Turai don zakulo wasu karin hanyoyin yakin da Boko Haram a Najeriya.