Najeriya: An kai hari a garin Sumaila

Harin yan bindiga a Najeriya Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Harin yan bindiga a Najeriya

A Najeriya rahotanni daga jihar Kano sun ce wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun kai hari Karamar Hukumar Sumaila a daren jiya.

Maharan dai sun kuma nufi ofishin 'yan sanda ne na garin kan babura, inda suka rika bude wuta.

Wasu mazauna garin sun ce karan harbe-harben ya tilasta musu barin gidajensu suna shiga daji, da kuma wasu garuruwa na kusa domin neman mafaka.

A nata bangaren rundunar 'yansandan jihar Kano ta ce babu asarar rayuka ko jikkata, don jami'anta sun maida martani nan take.

Ana dai danganta irin wadannan hare-hare da kai farmaki ne da 'yayan kungiyar Boko Haram dake ci gaba da yin barazana a wasu jihohin arewacin Najeriya.