Ayatolla ya ce 'yan Iraqi su dauki makamai

Wasu 'yan sa kai a Iraqi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dubban mutane ne suka tsere wa Mosul bayan masu fafutuka sun karbe iko da birnin

A Iraqi, malami mafi girma na 'yan Shi'a, Ayatollah Ali al-Sistani, ya yi kira ga 'yan kasar su dauki makamai domin yakar 'yan sunnu masu jihadi da ke barazanar afka wa Bagadaza.

A lokacin sallar Juma'a ne babban Ayatollah ya yi kiran da a dauki makaman.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, ta samu rahotannin da ke tabbatar da cewa masu kishin Islamar na kungiyar ISIS, sun hallaka fararen hula a birnin Mosul, wanda suka kwace a wannan satin.

Tun da fari Amurka ta ce tana duba hanyoyin taimaka wa gwamnatin Nuru al-Maliki na 'yan shi'a.

Karin bayani