'Yan gwagwarmaya na neman raba Iraqi

Yan gwarmaya a Iraqi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yan gwarmaya a Iraqi

Ana kara samun fargaba ta yiwuwar rabewar kasar Iraqi a yayinda 'yan Sunni masu tayar da kayar-baya ke kara dannawa tsakiyar kasar.

'Yan gwagwarmayar na kungiyar ISIS sun kwaci garuruwa a lardin Diyala na gabashin kasar - sun kuma ce daga nan sun doshi Bagadaza ne babban birnin kasar.

Yayinda aka tarwatsa mafi rinjayen sojan gwamnatin Iraqin, dakaru daga yankin Kurdawa mai dan kwar-kwaryar 'yancin gashin kansa sun mamaye sansanonin sojin da ake rikici kansu a lardin Kirkuk.

Masu aiko mana labarai sun ce ga alama kasar tana neman rabuwa ne zuwa bangarori na 'yan Sunni da Shi'a da na Kurdawa.

Shugaba Obama ya ce, yana duba yiwuwar matakai da daama da za a dauka wadanda suka hada da kai hari ta sama don taimaka ma gwamnatin Iraqi fatattakar masu tayar da kayar-bayan.

To amma jami'an Amurka sun yanke kaunar tura wasu sojoji zuwa kasar ta Iraqi.

Karin bayani