Sabon Sarkin Kano ya koma fada

Sarkin Kano mai martaba, Muhammadu Sanusi na II Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An yi ta cece ku ce game da rashin komawar sabon Sarkin fada

Sarkin Kano, Mai Martaba Malam Muhammadu Sanusi na II ya koma fada, bayan shafe kwanaki biyar ana zaman fadar a gidan gwamnatin jihar.

Sabon Sarkin ya jagoranci sallar juma'a a gidan gwamnati, inda a cikin hudubar da ya yi ya ce "An zabe ni ne ba don na fi kowa ba, idan na yi daidai a taimaka mini, idan na yi kuskure a gyara mini."

Mai Martaba ya kuma yaba wa marigayi Sarki Ado Bayero, inda ya yi alkawarin dora wa kan abubuwan da ya yi.

Mataimakin gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da wasu manyan jami'an gwamnati, da na fada kamar Wamban kano, Walin kano, Makaman gado da masu, kwamishinoni da malaman ne suka yi sallar juma'a a bayan sabon Sarkin.