Zagaye na 2 a zaben Afghanistan

Runfunan zabe a Afghanistan
Image caption Wannan shi ne zagaye na biyu na zabe a kasar.

A karo na biyu an bude runfunan zabe a kasar Afghanistan, domin sake zaben wanda zai maye gurbin shugaba Hamid Karzai.

A watan Aprilun da ya gabata ne aka gudanar da zabe wanda rahotanni suka bayyana cewa an tafka magudi,a wannan karon ma 'Yan takarar biyu wato Abdullah Abdullah da Asharaf Ghani za su sake fafatawa.

A makon da ya wuce ne Dr Abdullah ya tsallake rijiya da baya, bayan an kai masa hari, an kuma tsaurara matakan tsaro a runfunan zabe. Ya yin da Kungiyar Taliban ta yi barazanar wargaza shi.

A zabe na farko da aka yi Dr Abdullah na sahun gaba da gagarumin rinjaye, sai dai ana ganin a wannan makon Ashraf Ghani ke kan gaba.

A bangare daya kuma dukkannin 'yan takarar sun yi alkawarin yaukaka dangantaka da kasashen yamma, za kuma su yaki cin hanci da rasahawa a kasar.