Sabon Sarkin Kano yayi zaman fada a karon farko

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu
Image caption Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu

A karon farko, sabon Sarkin Kano, Mai Martaba Alhaji Muhammad Sanusi na biyu, ya gudanar da zaman fada a gidan sarautar.

A jiya da yamma ne sarkin ya shiga gidan sarautar bayan ya shafe kwanaki biyar yana zaune a gidan gwamnatin jihar, tun bayan nada shi.

Rahotanni sun ce a daukacin 'ya'yan marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero , sun je sun yi wa sabon sarkin mubaya'a, in banda Chiroman Kano, wanda suka nemi sarautar tare, wanda aka ce ya yi tafiya.

Shi ma Galadiman Kano, Alhaji Tijjani Hashim, ya halarci zaman fadar na yau.

Ana ganin wannan lamari, shi zai kawo karshen hatsaniyar da ta rika tasowa, bayan nadin sabon sarkin.