An kama dattawa 9 a Jihar Taraba

Hakkin mallakar hoto AP

Rahotanni daga Jihar Taraba a arewacin Najeriya sun ce jami'an tsaro sun kama wasu dattawa tara a garin Doshima dake Karamar Hukumar Ibi.

Dattawan da aka kaman dai Fulani ne, kuma kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah na zargin cewa sojoji ne da suka fito daga Jihar Filato, mai makotaka da Jihar ta Taraba, suka kama su a lokacin ake sallar juma'a.

To amma rundunar tsaro ta musamman mai aikin kiyaye zaman lafiya a jihar Filaton ta musanta hannun jami'anta a kamun.

Fulani makiyaya dai na kokawa ne da yadda suka ce sojojin suka yi dirar mikiya a masallacin juma'a na garin Doshiman, yayin da ake sallar juma'a, suka kama dattijan, kana suka tarwatsa sauran masu ibada.

Sakataren kungiyar Miyetti Allah a karamar hukumar ta Ibi, Alhaji Saidu Nyupka, ya ce lokacin da jami'an tsaron su ka je garin Doshiman, suna dauke da makamai, yayin da wani mutum guda da bai da kayan soji amma yana sanye da hular badda-kama, ya rika nuna wa jami'an tsaron wasu dattawa, inda suka kama mutane tara.

To amma kakakin rundunar tsaro ta musamman mai aikin kiyaye zaman lafiya a Jihar ta Filato, Captain Ikedichi Iweha, ya ce ba jami'ansu ne suka yi kamen ba.

Sai dai kuma kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Taraba, DSP Joseph Kwaji, ya ce sojoji ne suka yi kamen amma bai baba dai wani karin haske ba.

Kodayake dai Fulani makiyayan sun ce basu san dalilin da yasa sojojin daga Jihar Filato da suke zargin suka kama dattawan ba, to amma a makwannin baya, an samu wata matsala tsakanin Fulani da sojoji dake aiki a Jihar Filaton, inda sojojin suka zargi Fulanin da kashe wasu abokan aikinsu hudu a jihar suka tsallaka Taraba -- zargin da Fulanin suka musunta.

Daga bisani sojoji sun shiga Jihar Taraban, inda Fulanin suka zarge su da kona rugage fiye da arba'in na Fulani a cikin karamar hukumar Ibin.

To sai dai, a cewar sakataren kungiyar Miyetti Allah, ba sa da masaniyar cewa ko kama dattawan na da nasaba da wancan lamarin.

Ya ce idan ma akwai wani abu makamancin haka, to kamata yayi jami'an tsaron su bi ta hannun kungiyar Miyetti Allah domin tunkaratr lamarin, ba su yi gaban kansu ta hanyar far wa al'ummar Fulani ba.

Karin bayani