'Yan a-ware sun kakkabo jirgin Ukraine

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ma'aikatar tsaron dai ta mika sakon ta'aziyya ga iyalan sojojin da aka kashe.

Ma'aikatar tsaron Ukraine ta ce 'yan a-ware magoya bayan Rasha sun harbo daya daga cikin jiragen sufurinta a lokacin da ya ke kokarin sauka a filin jiragen sama na Luhansk da ke gabashin kasar.

Jirgin mallakar sojin saman kasar na dauke da dakaru kimanin 50 da kayayyaki a cikinsa a lokacin da aka harbo shi.

Jami'ai sun ce sojojin kasar ta Ukraine da dama sun mutu bayan harbo jirgin; kodayake ba su bayar da adadin sojojin da suka mutun ba.

Sojojin gwamnati ne ke da iko da filin jirgin amma galibin garin na Luhansk na hannun 'yan tawaye.

Karin bayani