Amurka na cigiyar shugaban Ansaru

Hakkin mallakar hoto AP

Amurka ta yi shelar bada ladan dala milyan takwas domin samun bayanai da zasu bata damar kama wasu mutane takwas da kira 'yan ta'ada a Afrika.

Na farko daga cikinsu shi ne Khalid al-Barnawi, dan Najeriya, wanda Amurkan ke zargin cewa shi ne shugaban kungiyar Ansaru, wadda ta samo asali daga kungiyar Boko Haram.

Sauran wadanda take cigiyar sune Hamad el-Khairy da Ahmed el Tilemsi na kungiyar MUJWA a Yammacin Afrika da kuma Abu Yusuf al-Muhajir wanda ake zargi da kai hare hare a kasar Masar.

Sanarwar da ofishin yada labarai na ma'aikatar harkokin wajen Amurkan ya bayar ta ce wannan na daga cikin matakin da kasar ke dauka na yaki da ta'addanci.

To amma a hirarsa da Sashen Hausa na BBC wani masanin harkokin tsaro a Najeriya, Dokta Bawa Abdullahi Wase, yace wannan matakin ba zai yi tasiri ba.

Yace a bara ma gwamnatin Amurkan ta yi irin wannan shelar amma bata samu nasarar kama kowa ba.

Ga cewarsa, idan da shelar bada la'ada ko aiki da karfin soji na magance matsalar ta'addanci, to da abin da ke faruwa a Iraki a yanzu -- inda mayaka 'yan Sunni masu kaifin kishin Islama suka kame wasu birane -- ba zai faru ba.

Dokta Wase yace bin tafarkin sulhu da tattaunawa da 'yan gwagwarmaya sune hanyoyi masu tasiri wajen warware matsalar ta'addanci.

Karin bayani