Amurka da Iran za su tattauna kan ISIS

Mayakan kungiyar ISIS Hakkin mallakar hoto AP
Image caption ISIS dai na kokarin kafa kasar musulunci a Syria da Iraqi

Kasar Amurka na duba yiwuwar bude tattaunawar kai tsaye da Iran kan halin rashin tsaron da ake ciki a kasar Iraki.

Wani jami'n Amurka ya shaidawa BBC cewa manyan jami'an amurka sun yi nazari kan yiwuwar tattaunawar da Iran, wasu rahotannin na cewa ta yiwu a fara a cikin makon nan.

Idan har Amurka da Iran su kai wannan tattaunawar, hakan wani gagarumin ci gaba ne tsakanin kasashen da suka shafe tsawon lokacin su na 'yar tsama.

Washington dai ta sha nanata zargin Iran da haddasa rikicin da ake yi a Iraqi, sai dai duka bangarorin biyu na da muradin hana mayakan sa kan sake kwace iko da karin wasu yankuna.