John Kerry ya yi kira ga gwamnatin Iraqi

Shugaban kasar Iraqi Nouri al-Maliki Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu tada kayar baya sun dade su na kai hare-hare a sassa daban-daban na kasar Iraqi.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya shaidawa gwamnatin Iraqi cewa idan har ana son taimakon da Amurka zata bada na magance matsalar masu tada kayar baya a cimma nasara, dole ne shugabanin kasar su jingine banbance-banbancen da ke tsakaninsu

John Kerry ya shaidawa Prime Ministan Iraqi cewa ya kamata gwamnatin ta 'yan Shi'a ke jagoranta ta mutunta hakkin 'yan kasar da suka hada da Kurdawa, da mabiya darikar Sunni da Shi'ar, tare da bukatar gwamnati ta gudanar da zabe ba tare da bata lokaci ba.

Amurka ta kai wani jirgin ruwa da ke jigilar jiragen yaki zuwa yankin gulf, a matsayin martani ga sabon rikicin da ya barke a daidai lokacin da masu tada kayar baya suka karbe iko da wasu sassan kasar.