Ana kokawa da shirin rusa kasuwanni a Bukuru

Hakkin mallakar hoto plateau state govt
Image caption Sun bayyana cewa matakin gwamnatin ya keta hakkinsu na ‘yan kasa.

Dubban 'yan kasuwa da masu gidajea yankin Bukuru na jihar Filaton Najeriya na kokawa da yunkurin da gwamnatin jihar ke yi na rusa kasuwanni da wasu gidaje a yankin.

Bayanai dai na cewa gwamnatin na shirin ruguza wasu manyan kasuwanni biyu ne da kuma gidaje da dama a yankin; domin gina filin wasanni da kuma hanyar mota.

Sai dai wadanda da lamarin ya shafa na cewa gwamnatin na yi masu kora da hali ne kuma matakin zai jefa su cikin kuncin rayuwa.

Kodayake kwamishinar watsa labarai ta jihar Filaton Mrs Olivia Daziem, ta bayyana cewa manufar gwamnati ita ce kawo ci gaba ga jama'ar yankin, amma ba jefa su cikin wahala ba.

Karin bayani