Tsofaffin ma'aikatan Areva sun koka

Ma'aikatan kamfanin Areva da suka gudanar da zanga-zanga kwanakin baya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ma'aikatan kamfanin Areva sun gudanar da zanga-zanga kwanakin baya

A Jamhuriyar Nijar Kungiyar tsoffin ma'aikatan hakar ma'adinai ta koka a game da abin da ta kira halin ko in kula da kamfanin Areva ke nuna wa tsofin ma'aikatansa da iyalansu da zaran sun kamu da wata cuta mai nasaba da hakar uranium.

A cewar kungiyar 'ya'yanta ba su samun kulawa ta fannin kiwon lafiya daga kamfanin, abin da ya saba wa alkawuran da ta dauka.

Sai dai gwamnatin Nijar da kamfanin na cewa ba gaskiya ba ne don kuwa akwai tsarin kula da lafiyar ma'aikatan da iyalansu.

Malama Bibatu Haruna Kailu ta bayyana cewar ana yin shakulatun bangaro da lamurran lafiyar ma'aikatan hakar ma'adinan da iyalansu, sanann babu wani tallafi da ake bayar wa ga iyalan wadanda suka rasu sanadiyyar hakar ma'adinin Uranium.