Najeriya: An gano bam a cocin jihar Imo

Image caption 'Yansanda dai sun ce suna ci gaba da yi wa mutanen tambayoyi.

'Yansanda a kudu maso gabascin Najeriya sun kama wasu mutane biyar dangane da gano wani abu da ake jin bam ne a wani coci da ke birnin Owerri na jihar Imo.

An dai gano abin ne kunshe a cikin buhu wanda aka ajiye a kofar shiga cocin Winners' Chapel reshen birnin na Owerri ranar Lahadi.

'' A duk sa'adda irin wannan abin ya faru to dole ne a yi kame domin samun bayanan da za su kai ga zakulo wadanda suka kitsa wannan abu,'' inji Mai magana da yawun 'yansanda a jihar Dsp Andrew Enwerem.

Wani wakilin BBC a yankin ya ce tuni dai 'yansandan suka lalata abin da aka gano din, tun kafin ya kai ga fashewa kuma suka dauki matakan tsettsefe wuraren ibada da sauran wuraren hada-hadar jama'a a birnin na Owerri, don a tabbatar da cikakken tsaro.

Karin bayani