An kashe dan Taliban da ya yanke yatsun mutane

Wasu 'yan Afghanistan da aka yanke wa yatsu Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan takarar sun yi alkawarin kyautata dangantaka da kasashen yamma tare da yaki da rashawa

'Yan sanda a Afghanistan sun ce an kashe kwamandan Taliban da ake zargi da yanke yatsun wasu mutane 11 da suka yi zabe.

Jami'an sun ce an harbe Mullah Shir Agha da wani dan fafutuka a wani farmakin da aka kai a yammacin lardin Herat.

Ana zargin kwamandan da yanke wa mutanen yatsun da suka yi dangwale da shi a zaben shugaban kasar da aka yi a ranar Asabar a Afghanistan.

Kungiyar ta Taliban ta lashi takobin hana zaben zagaye na biyu tsakanin tsohon ministan wajen kasar Abudallh Abdullah da kuma ministan kudi Ashraf Ghani.