Ana tsare da 'yan arewa kan Boko Haram

Image caption Haka ma wani shugaban al'umma da ya je barikin domin belin mutanen bai dawo ba

Hukumomin soja na ci gaba da tsare mutanen nan fiye da dari hudu da suka kama a garin Aba na jihar Abiya, bisa zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne.

Wani mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya, Birgediya Janar Olajide Laleye, ya tabbatar da batun kama mutanen, wadanda suka fito daga jihohin arewacin kasar, irinsu Jigawa da Bauci, a cikin motoci bas-bas talatin da shida, a kan hanyarsu ta zuwa birnin Fatakwal na jihar Ribas.

Sai dai kuma wasu na ganin wannan kame, yana tattare da nuna wariya da tsangwama ga 'yan arewacin Najeriya a kudancin kasar.

Bayanai sun ce galibin mutanen 'yan asalin jihar Jigawa ne masu zuwa birnin Fatakwal na jihar Ribas, domin gudanar da harkokin kasuwanci da kuma ci-rani.

Wani wakilin BBC a yankin ya ce sojojin sun kama mutanen ne cikin motocin bas-bas 36 a kusa da garin Aba kan babbar hanyar zuwa Fatakwal.

A farkon wannan shekarar ne 'yan sanda a jihar ta Ribas suka tsare wasu 'yan Jigawa kimanin 300, bisa zargin cewa 'yan kungiyar ta Boko Haram negerger, amma daga bisani aka sake su.

Karin bayani