Fada ya sake barkewa a Iraqi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rikicin da Iraqi ke fuskanta na neman raba kasar gida biyu.

Fada ya barke tsakanin jami'an tsaron Iraqi da masu tada kayar baya 'yan Sunni da suka fara kaddamar da hare-haren a makon da ya wuce.

Rahotanni sun ce 'yan tawayen sun karbe iko da wasu sassan birnin Baquba mai nisan kilomita shida daga birnin Bagadaza.

Can arewacin Iraqi kuma, dakarun gwamnati ne ke kokarin karbo garin Tal Afar da 'yan tawayen suka karbe a jiya litinin.

A yammacin birnin Bagadaza kuwa, masu tada kayar bayan sun kakkabo jirgin gwamnati a kusa da yankin Falluja, sun kuma ce sun lalata tankokin yaki mallakar gwamnati.

Shugaba Obama yace, Amurka za ta tura dakarun soji dari biyu da saba'in da biyar kasar Iraqi domin kare ofishin jakadancin Amurka da Amurkawa dake zaune a Bagadazan.

Karin bayani