Al Shabab ta kai wani sabon hari a Kenya

Al Shabab ta kai wani hari
Image caption Harin Al Shabab a Kenya

Kungiyar masu zafin kishin Islama ta Al Shabab ta kaddamar da wani sabon hari a gabar tekun kasar Kenya inda ta hallaka mutane akalla 20.

Wani mai magana da yawun kungiyar ya ce wadanda aka kashe sun hada da jami'an yan sanda da ma'aikatan gandun daji.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce 'yan bindigar sun kai harin ne kan wasu kauyuka da ke yankin Poromoko a gab da garin Mpeketoni inda 'yan kungiyar Al Shabab suka kashe mutane 48 ranar lahadi da dare.

Kungiyar Al Shabab ta ce ta kai hari ne domin maida martani akan mamayen da Kenya ta yiwa Somalia da kuma cin zarafin da ake yiwa musulmai a Kenya.

Kenya ta tura sojoji zuwa Somalia ne a shekara ta 2011.