Mutane 30,000 na gudun hijira a Maiduguri

Wasu 'yan gudun hijira a Maiduguri Hakkin mallakar hoto NEMA
Image caption A lokuta da dama maharan kan kona kasuwanni tare da sace kayan abinci ko ababen hawa

Hukumar agajin gaggawa ta Nigeria, NEMA ta ce mutane fiye da 30,000 ne ke gudun hijira a birnin Maiduguri a jihar Borno.

A cewar hukumar mutanen sun rasa matsugunansu ne a yankunan Alau da Gwoza da kuma kewayen Maiduguri, inda ake samun hare-haren Boko Haram.

Hukumar ta bayyana fatan kafa sansanin 'yan gudun hijira a birnin na Maiduguri, idan har ta samu tabbacin tsaro daga jami'an tsaro.

Ana dai zargin 'yan Boko Haram da kai hare-hare ba kakkautawa a kauyuka da garuruwa tare da kona gidaje da dama, inda a wasu lokuta maharan kan kona daukacin kauye ko gari a jihar ta Borno a baya-bayan nan.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba