Shafin PayPal ya bude reshe a Nigeria

Shafin intanet na PayPal
Image caption PayPal zai bai wa masu asusu da shi damar biyan kudade ta hanyar wayoyin salula ko kwamfutarsu

Shafin intanet na PayPal da ke bude asusun intanet ga mutane, domin biyan kudi ga shagunan sayar da kayayyaki na intanet ya fara aiki a Nigeria.

A ranar Talata ne Paypal ya fara aiki a Najeriya, wadda tana cikin kasashe 10 da PayPal ya fara aiki a cikinsu a wannan makon.

Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ambato shugaban Paypal na yankin EMEA, Rupert Keeley na cewa, fadada harkokinsa a kasashen 10 zai kawo jimillar kasashen da yake aiki zuwa 203 a duniya.

Da zarar shafin na PayPal wanda reshe ne na eBay ya fara aiki a kasasehn 10, duk wanda yake da damar shiga intanet, kuma yake da katin banki da za a iya sayayya da shi a intanet, zai iya rajista domin samun asusun PayPal.

Kuma da asusun na PayPal ne mutum zai iya biyan kudi ga miliyoyin shagunan intanet a fadin duniya.