Cutar Ebola ta kashe mutane 337

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cutar Ebola ta yi barna sosai a kasar Guinea

Cutar Ebola da ta barke tun a watan Fabarairu a yankin yammacin Afrika ta hallaka mutane 337.

Hukumar lafiya ta duniya, WHO wacce ta fitar da wannan sabon adadin ta ce hukumomin lafiya a kasashen sun kasa shawo kan cutar.

Cutar wacce ta barke a kasar Guinea ita ce bala'i mafi muni game da ita a tarihi.

Cutar ta kuma yadu zuwa kasashen Saliyo da kuma Liberia.

A makon da ya gabata an samu karin mutane da suka kamu da cutar.

kwayar cutar Ebola ba tada rigakafi kuma tana janyo zazzabi mai zafi da kuma zubar jini.

Karin bayani