Iraqi ta nemi taimakon Amurka

Nouri al-Maliki Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Nouri al-Maliki, Pirayim Ministan Iraqi

Gwamnatin Iraqi ta bukaci taimakon Amirka a hukumance, da agaji ta mayakan sojin sama a gumurzun da take yi da mayakan jihadi na Sunni.

Babban kwamandan sojin Amirka Janar Martin Dempsey ya tabbatar da bukatar ta Iraqi.

Sai dai bai yi wani karin haske ba akan ko Amirkar za ta yi wani abu akai.

A makon da ya wuce shugaba Obama yace yana nazarin matakin da Amirkar za ta dauka.

Tun da farko Firaministan Iraqin Nouri al Maliki ya yi kokarin karfafa karsashi da cewa gwamnatinsa na shirin kaddamar gagarumin farmaki domin koyawa masu Jihadin darasi.

A bangare guda kuma 'yan sunni masu fafutuka sun kai hari kan babbar matatar mai da ke Baiji a Iraqi.

An samu rahotanni masu karo da juna da ke cewa masu fafutukar sun karbe iko da kusan baki dayan matatar bayan kashe masu gadi.

Amma wasu majiyoyi na gwamnati sun gaya wa BBC cewa har yanzu matatar na karkashin ikon dakarun tsaro.

Rahotanni na cewa sojojin Iraqi sun tura wani jirgi mai saukar ungulu mai bindigogi , inda jirgin ya harba makami mai linzami kan wani tankin mai, abin da ya janyo gobara.