An kashe Mutane da dama a harin bam na Yobe

Wurin da aka kai hari a Damaturu Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wurin da aka kai hari a Damaturu

Wani bam ya fashe a arewa maso gabashin Nijeriya a wani wuri da masu sha'awar kallon kafa ke kallon gasar wasan kwallon kafa ta duniya.

An ba da rahoton cewa an kashe mutane da dama.

Mutanen da suka shaida lamarin sun ce wani dan kunnar bakin wake ne a cikin keken Napep ya tayar da bam din a garin Damaturu na jihar Yobe.

Ma'ikatan kiwon lafiya sun ce an kai mutanen da suka jikkata cike a manyan motoci a asibitin.

Wani mutum wanda ya shaida lamarin ya gaya ma BBC cewar ba za a iya kiyasin mutane da suka mutu ko suka jikkata a wurin ba.

A ranar alhamis hukumomi a jihar Adamawa dake arwa maso gabashin Nijeriyar suka ba da umurnin a rufe dukkan cibiyoyin dake shirin nuna gasar kwallon kafar, saboda barazanar da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi ta kai hari.

Karin bayani