Nigeria ta sa $20m don tsaron makarantu

Image caption Za a samar da ruwan sha da ababen more rayuwa tare da inganta gidajen malaman makaranta a karkashin shirin

Gwamnatin Nigeria da wasu manyan 'yan kasuwa kamar Alhaji Aliko Dangote sun sanya dala miliyan 20 domin samar da tsaro a makarantu.

Ministar kudi ta Nigeria Dr. Ngozi Okonjo Iweala ta ce ana bukatar dala miliyan 100 ne domin aiwatar da shirin inganta tsaro a daukacin kasar baki daya.

Sai dai ta ce shirin zai fara ne da makarantun da ke yankin arewa-maso-gabashin kasar, saboda tashe-tashen hankulan da ake fuskanta.

Wakili na musamman na Majalisar Dinkin Duniya a kan Ilimi, Gordon Brown ya ce nan da 'yan makonni ne kasashen yamma kamar su Burtaniya da Amurka da Norway za su sanar da gudunmawar da za su bai wa Najeriya game da shirin.