An soki Nigeria kan janye tuhumar Abacha

Hakkin mallakar hoto nigeria at 50
Image caption Gwamnatin na zargin tsohon shugaban da satar kudin ne a lokacin da yake mulki tsakanin 1993 zuwa 1998.

Ana ci gaba da sukar lamirin gwamnatin Najeriya a kan janye tuhumar almundahana da take yi wa dan tsohon shugaban kasar na soja janar Abacha.

Masu sukar sun bayyana cewa matakin ya kara tabbatar da cewa gwamnatin ba dagaske take ba wajen yaki da rashawa a kasar.

Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta kasar, APC, na jihar Kano Alhaji Haruna Umar Doguwa, ya ce yana ganin gwamnatin ta yi haka ne saboda Muhammad Abacha ya shiga jam'iyyar PDP.

A da gwamnatin tana tuhumar dan tsohon shugaban ne da karbar dukiyar sata ta biliyoyin naira.