Amurka ta rage sayen mai daga Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Satar danyen mai da ma'aikatan ga rashin tsaro na cikin dalilan da wasu ke ganin ya sa Amurka ta rage sayen mai a Nigeria

Amurka ta yi matukar rage yawan danyen man da take saya daga Najeriya, abin da ya sa a yanzu Indiya ta zama kasar ta da fi kowacce sayen danyen mai daga Nigeria.

A yanzu dai Amurka na sayen gangar danyen mai 250,000 a rana daga Najeriyar.

Amurka dai ta fara hako danyen mai a kasarta, ko da yake wasu na ganin dalilai na tsaro na cikin abubuwan da suka sa Amurka ta rage sayen danyen mai daga Najeriya.

Indiya kuwa a yanzu tana sayen kashi 30 cikin dari na gangar danyen mai fiye da miliyan biyu da ake hakowa kullum a Najeriya.

Kasashen China da Malaysia ne ke rufawa Indiya baya wajen yawan danyen man da suke saya a Najeriya.

Karin bayani