Amurka za ta tura mashawartan soji Iraqi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Obama ya ce ana iya magance matsalolin Iraqi ta hanyar siyasa

Shugaban Amurka Barak Obama ya ce kasar za ta aike da jami'an soja mashawarta fiye da dari uku don tallafa wa gwamnatin Iraqi wajen magance barazanar 'yan tada-kayar-baya da suka kwace iko da yankunan kasar.

Da yake gabatar da jawabi a fadar White House, Obama ya ce Amurka za ta yi shirin daukar wani matakin soja takaimaimai a kan wasu yankuna, idan akwai bukatar haka.

Ya jaddada cewa dakarun Amurka ba za su koma Iraqi da sunan mayaka ba. Ya ce ba hurumin Amurka ba ne ta zaba wa Iraqi shugabanni, sai dai ya ce masu manufar damawa da kowanne bangare ne kadai za su yi nasarar tsamo Iraqi daga rikici.

'yan siyasar Amurka da dama ne ke ta kiraye-kiraye ga Firaministan Iraqi Nouri al-maliki ya yi murabus, yayin da Obama ke nanata cewa ana iya magance matsalolin Iraqi ne kadai ta hanyar Siyasa.

Ya kuma sanar cewa zai tura Sakataren harkokin wajensa, John Kerry a karshen wannan mako don gudanar da tattaunawa kan wannan rikici da shugabannin Turai da na kasashen gabas ta tsakiya.