Rayuwar 'yan gudun hijira a Diffa

Hakkin mallakar hoto

'Yan gudun hijira kimanin dubu arba'in ne ke zaune a jihar Diffa ta jamhuriyar Nijar bayan tsere wa rikicin Boko Haram daga Nigeria.

Wasu daga cikin masu gudun hijirar maza da mata da kananan yara 'yan asalin Nijeria da Nijar da suka tsere wa rikice-rikicen Boko Haram na samun tallafi daga kungiyoyin ba da agaji na cikin gida na da duniya.

Kungiyoyin agaji da suka hadar da Hukumar samar da abinci ta duniya da kungiyar ba da agaji ta Geneva suna kokarin tallafa wa 'yan gudun hijirar da kayan abinci da sauran kayan masarufi.

Ali Zubairu jami'in kula da jama'a ne na daya daga cikin irin wadannan kungiyoyin agaji a jamhuriyar Nijar ya ce 'yan gudun hijirar suna cikin tsananin bukata.

Sai dai yayin da wasu ke san-barka da tallafin da suke samu, wasu 'yan gudun hijirar a sansanin garin Diffa sun ce shafe kusan wata biyu amma har yanzu ba su iya samun taimako ba.