Abacha: Za a dawo wa Nigeria da $227m

Image caption Gwamnatin Nijeriya ta ce za ta sa kudin a asusun zuba jari na kasar

Ma'aikatar kudi ta Nigeria ta ce Gundumar Liechtenstein za ta dawowa da kasar $227m da tsohon shugaban mulkin sojan kasar Sani Abacha ya wawashe a shekarun 1990.

Ta ce matakin wani yunkurin shekaru 16 ne don ganin an dawowa da Nijeriya kudi.

Tun da farko, gwamnatin Nijeriya ta amince ta janye tuhumar tafka almundahana da take yi wa Iyalan Janar Abacha.

Sani Abacha ya mulki Nijeriya daga shekarar 1993 ya zuwa mutuwarsa a 1998 kuma ana tunanin ya wawashe biliyoyin daloli inda ya kai asusun ajiya na kasashen waje a fadin nahiyar Turai.

Kungiyar Transparency International ta ce Dan mulkin kama karyan ya sace kimanin dalar Amurka biliyan biyar a tsawon mulkinsa.

Sanarwar da Ma'aikatar kudin kasar ta fitar ta ce tana da tabbacin cewa a ranar 25 ga watan Yunin bana Nijeriya za ta karbi $227m daga gwamnatin gundumar Liechtenstein, a matsayin wani bangare na dukiyar da aka karbo a wajen iyalan Abacha.