Masu fafutukar Islama na barazana a Afrika

Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Sai dai rahoton ya yi ayar tambaya game da ko Majalisar za ta iya magance matsalar a yankin

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, tashe-tashen hankula masu alaka da 'yan gwagwarmayar Musulunci a arewacin Afirka na yin barazana ga zaman lafiya a daukacin yankin.

Majalisar ta ce kasashen da lamarin ya fi shafa sun hada da Najeriya da Libya da kuma Mali.

Wani rahoto na kwamitin tsaro na majalisar ya bayyana cewa, ayyukan ta'addanci a yankin Sahel da na Maghreb sun karu sosai da kashi sittin cikin dari a shekarar 2013.

Rahoton ya kara da cewa, matsanancin talauci na kara dagula al'amarin da kuma rashin aikin yi a tsakanin matasa wadanda su ne aka fi cusawa tsatsauran ra'ayin Musuluncin.