Masar: An yanke wa mutane 180 hukuncin kisa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane da dama sun yi Allah wadai da hukuncin kisan

A Masar wata kotu ta tabbatar da hukuncin kisan da aka yanke wa 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi da aka haramta su dari da tamanin.

Wadanda aka yankewa hukuncin dai suna cikin mutane kusan dari bakwai da aka zarga da kai hari akan wani ofishin 'yan sanda dake garin Minya.

Harin da yayi sanadiyyar mutuwar dan sanda guda.

Wau dangin wadanda aka yanke wa hukuncin sun yi Allah wadai da lamarin.