'Yan Boko Haram sun kai hari a Borno

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abubakar Shekau na Boko Haram

Rahotanni daga jihar Borno da ke arewacin Nigeria na cewar 'yan Boko Haram sun kai hari a kan wani kauyen Koronginim da ke kusa da garin Chibok.

Wani mazaunin kauyen ya shaidawa BBC cewar an kashe mutane uku a harin sannan kuma an kona kauyen kurmus.

Kauyen Koronginim na makwabtaka da garin Chibok inda 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata dalibai fiye da 200 fiye da makonni tara da suka wuce.

Haka kuma wasu bayanai sun nuna cewar 'yan Boko Haram sun yi awon gaba da wasu maza da 'yan mata a kauyen Yaza na jihar ta Borno.

Kungiyar Boko Haram na cin karenta ba babbaka a kauyen jihar Borno da ke karkashin dokar ta-baci fiye da shekara guda da ta wuce.

Karin bayani