Za a ci gaba da shari'ar Shell da Bodo

Image caption Al'ummar Bodo sun ce cin fuska ne gare su, Shell ya tunkare da su da 'yar wannan diyya

Kamfanin hakar man fetur na Shell ya ce tayin fam miliyan 30 da ya yi wa al'ummar Bodo a yankin Neja-Delta tun bara don cimma masalaha a shari'arsu, na nan daram.

Kamfanin lauyoyi na Leigh Day ne ya shigar da kara a London cikin 2011 a madadin al'ummar Bodo da ke Nijeriya inda ya bukaci Shell ya biya diyyar fam miliyan 300 saboda tsiyayar mai sau biyu da ta gurbata muhallinsu.

Babbar kotun London a wani hukuncin share fage, ta ki amincewa da bukatar biyan fam miliyan 300.

Leigh Day ya ce hukuncin muhimmi ne ga wadanda yake tsayawa don kuwa ya bayyana Shell a matsayin wanda ke da alhakin karewa da yi wa Bututunsa garkuwa.