Yaki da shan sukari a Birtaniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sukari na janyo kiba sosai ga yara

An bukaci Gwamnatin Burtaniya data kirkiro da wani haraji akan amfani da sukari domin dakile yawan kiba tsakanin kananan yara.

Wata kungiyar yaki da shan sukari ce ta samar da wasu shirye shirye guda bakwai da nufin karya kwarin gwiwar Yara kanana daga cin abinci da kuma lemuka dake dauke da sukari mai yawa a cikinsu.

Kungiyar tana kuma son ganin an dakatar da kamfanonin dake samar da abinci mai yawan sukari a ciki daga daukar nauyin wasanni.

Kashi 14 cikin 100 na Yara kanana a Burtaniya masu shekaru 2 zuwa 15 na fama da matsalar kiba mai yawa.

Kungiyar tace wannan ka iya haifar da cututuka da suka hada da na zuciya, wadanda suke sauran kisa da kuma nakasa mutum a cikin kasar