Shugaban Tunisiya na ziyarar Nijer

Hakkin mallakar hoto AP

Shugaban kasar Tunisiya Moncef Marzouki ya kai ziyara a Jamhuriyar Nijer ranar Lahadi, a wani kokarin bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

A ziyarar ta yini daya dai shugaban Tunisiyan ya tattauna da Shugaban Nijar Mouhammaduu Isoufou kan hanyoyin farfado da hulda tsakanin kasashen biyu.

Shugaban Marzuki ya je ne tare da babbar tawagar da ta hada da 'yan kasuwa da manyan jami'an gwamnati.

Sun kuma tattauna da 'yan kasuwa da jami'an gwamnatin Nijar game da batun saka jari a kasar ta Nijer.

Kasashen biyu kuma sun tattauna akan batun tsaro, inda suka yi batun hadin kai domin yaki da ta'addanci.

Wannan ne dai karo na farko a cikin shekaru 40 da wani shugaba na Tunisiya ya kai ziyara a Nijer.

Karin bayani