Boko Haram sun kai hare-hare a Borno

Hakkin mallakar hoto AFP

A Najeriya, 'yan kungiyar Boko Haram sun kai hare-hare a kudancin Jihar Borno, inda rahotanni suka nuna cewa harda harin kunar bakin wake a garin Gwoza.

Kamfanin dillacin labarai na AFP yace harin kunar bakin waken ya halaka sojoji ukku ya kuma jima wasu sojoji ukku raununa.

Kamfanin ya ruwaito cewa an kai harin ne a ranar Lahadi a wurin da sojoji ke binciken ababen hawa a garin Gwozan.

A ranar Asabar ma 'yan Boko Haram sun kai hare-hare a kauyukan Kwarangilam da Yaza a kudancin Jihar Bornon.

Wani wanda ya ganewa idonsa kuma ya rasa dan uwa daya daga cikin hare-haren ya ce ya ga gawawaki kusan 40.

Kauyukan dai na kusa da garin Chibok ne inda 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata sama da 200 fiye da watanni biyun da suka gabata.

Karin bayani