Abbot ya roki Al-Sisi ya saki Peter Greste

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana tsare da Peter Greste da wasu a Masar tun watanni shidan da suka gabata

Fira Ministan Australia Tony Abbot ya yi wani roko na kai tsaye ga Shugaban Masar Abdul Fatah Al Sisi, na sakin ma'aikacin gidan Talabijin na Al Jazeera Peter Greste.

Yayinda yake magana ga rediyon ABC, Mr Abbot ya ce ya bayyanawa Shugaban Masar cewa Mr. Greste bashi da laifi

Mr. Greste wanda dan Australia ne, na daya daga cikin ma'aikatan gidan Talabijin din Al Jazeera da suke tsare a Masar, tun watanni shidan da suka gabata.

Ana zarginsu da yayata labarai na karya, da kuma hadin baki da kungiyar 'yan uwa musulmi ta tsohon Shugaba Mohammed Morsi.