Mahimmacin Dazuka ga rayuwar dan Adam

Hakkin mallakar hoto CEJL
Image caption 'Bishiyoyi na samar da abinci da man fetur da kuma kudaden shiga kai tsaye'.

Wata babbar jami’ar majalisar dinkin duniya ta bayyana dazukan duniya da cewa suna da mahimmanci ga rayuwa da kuma jin dadin dan Adam

Eva Mueller, ta ce bishiyoyi na samar da abinci da man fetur da kuma kudaden shiga kai tsaye.

Majalisar dinkin duniya ta fitar da wani rahoto kan halinda dazuka ke ciki a Rome kasar Italiya

Jami’ar ta kara da cewa abincin da ake samu daga dazuka irinsu ‘ya’yan itatuwa da ganyayyaki da kwari da kuma namun daji a wasu lokuta na samar da kayan abinci masu gina jiki ga mutanen karkara

Rahotan wanda aka wallafa shi a lokacin da aka fara taron mako guda na majalisar dinkin duniya akan dazuka, ya ce lokaci ya yi ga wannan bangare ya karkata zuwa mutane a madadin bishiyoyi.