Gwamnatin Kano ta yi tur da harin bam

Image caption Kimanin mutane 20 ne kuma suka jikkata a hari na ranar Litinin

Gwamnatin jihar Kano ta yi tur da harin da aka kai Kwalejin koyan aikin kiwon lafiya, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutune takwas.

Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana harin da cewa wani sabon lamari ne dake bukatar jama'a su kasance masu sa-ido.

Sai dai ya yi tsokaci game da sakacin masu gadi, wanda ya ce da sun duba watakila da an kauce wa aukuwar harin.

Kawo yanzu babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, amma a baya kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare a jihar.