Rikicin Iraqi: Kerry ya isa Bagdaza

Mr. Kerry da al-Maliki Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana sa ran Mr. Kerry zai yi kira da a kafa gwamnatin hadin kan kasa a Iraqi

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya isa Bagdaza babban birnin Iraqi, a lokacin da rahotanni ke cewa mayakan sunni na samun galaba.

Rahotanni sun nuna cewa masu tayar da kayar bayan na kokarin karbe iko da wata madatsar ruwa mai samar da wutar lantarki da ke kusa da birnin Haditha.

Mr. Kerry ya gana da Firai minista Nouri Al Maliki, kuma ana sa ran zai yi wata ganawar da shugabannin Sunni da na 'yan Shi'a da kuma na Kurdawa.

A ranar Lahadin da ta wuce ne mayakan da kungiyar ISIS ke jagoranta suka karbe iko da bakin iyakar kasar ta bangaren Syria da Jordan.