Dambarwa game da tsige Murtala Nyako

Image caption 'Yan majalisa na son a sanar da tsige gwamnan ta kafafen yada labarai

A Najeriya ana cigaba da dambarwa a jihar Adamawa game da yunkurin tsige gwamnan jihar da wasu 'yan majalisar ke yi.

Majalisar ta sake zartar da wani kudiri daya baiwa Akawunta ikon sanar da Gwamnan da mataimakinsa sanarwar shirin tsige su ta kafafen yada labarai, bayan Akawun ya kasa cim musu domin ya mika musu hannu da hannu.

Sai dai Gwamnan a nasa bangaren, ya zargi 'yan majalisar da sabawa ka'ida, don haka ya ce ba zai saurare su ba.

Jahar Adamawa dai na daya daga cikin jahohin arewa maso gabashin Nigeria dake karkashin dokar ta baci.