Kotu a Sudan ta saki matar da ta yi ridda

Meriam da mijinta
Image caption Matar ta haifi 'ya mace a lokacin da take kurkuku

Wata kotu a Sudan ta ba da umarnin sakin wata mata da aka yanke wa hukuncin kisa, saboda ridda.

A watan jiya ne wata kotun shari'ar Musulunci ta yanke wa Meriam Ibrahim hukuncin kisan, tare da bulala 100 saboda zaman zina da ta yi na auren wani Kirista.

Sudan ta dauki Meriam Musulma saboda babanta Musulmi ne kuma a hannunsa ta girma, amma shari'arta ta janyo suka daga kasashen duniya.

Lauyan da ke kare ta ya shaida wa BBC cewa an sake kuma yana kan hanyarsa na zuwa wurinta.