Daliba mai shekaru 15 na karatun digiri na 3

Image caption Yawancin mutane sun yi mamaki da nuna rashin yarda da jin wannan labarin.

Jami'ar Leicester da ke Burtaniya ta ce tana da daliba mai karancin shekaru, wadda ke karatun digirinta na uku.

Eugenie De Silva mai shekaru 15 na karatu ne a sashen kimiyyar siyasa, kuma taken nazarinta shi ne ''Musu da yaudarar da ke cikin Yakin Duniya na biyu'' a karatun nata na zama dakta.

Yarinyar dai tana zaune ne a jihar Tennessee ta Amurka, amma za ta yi karatun digirin nata na uku daga gida.

Wanda zai duba rubuce-rubucenta, Farfesa Mark Phythian ya ce babu shakka game da ko za ta iya karatun digirin na uku.

Karin bayani