An tafka sata a wani Bankin Turai

Image caption Mutanen da abin ya shafa sun fito ne daga Italiya da Turkiyya

Wani kamfanin samar da Tsaro ya bada rahotan cewa wasu masu satar bayanan Intanet sun yiwa wasu kwastomomi su fiye da 190 dake hulda da wani bankin Turai sata

Kamfanin mai suna Kaspersky Lab yace ya gano rumbun adana bayanai na wata Kwompita a watan Janairu da aka yi amfani da shi wajen satar dala 700,000 a cikin mako guda

Kamfanin ya ce ya yi imanin cewa da dama daga cikin masu ajiya a bankin wadanda aka yiwa satar na Kasashen Italiya da kuma Turkiyya

Kamfanin ya ce ya sanar da hukumomi game da wannan matsalar.

Sai dai ya kara da cewa masu aikata laifin sun yi kokarin goge duk wata hujja da za a iya amfani da ita wajen gano su kafin a san ko su wanene

Kamfanin dai ya ki bayyana sunan bankin da wannan al'amari ya shafa