An sake sace mata 60 a jihar Borno

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasashen duniya sun kawo wa Nigeria dauki domin magance matsalar Boko Haram tare da gano 'yan Chibok

Wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun sace mata da kuma wasu 'yan mata fiye da 60 a jihar Borno da ke arewa-maso-gabashin Nigeria.

Al'amarin ya faru ne a lokacin wasu jerin hare-haren da ake zargin 'yan kungiyar da kai wa a kauyen Kummabza a makon jiya.

Dan majalisar dattawa mai wakiltar kudancin Borno, Sanata Ali Ndume ya tabbatar da aukuwar lamarin, ko da yake ya ce ba zai iya tabbatar da adadinsu ba.

Fiye da watanni biyu kenan da aka sace 'yan mata 'yan makaranta fiye da 200 a garin Chibok, kuma kawo yanzu babu duriyarsu.