Nigeria: Ce-ce ku-ce game da katin shaida

Image caption Wasu 'yan arewa mazauna Imo sun bayyana damuwar su

A Najeriya, an shiga ce-ce-ku-ce game da wani tsarin samar da katin shaida, wanda aka ce an bullo wa da 'yan arewacin Kasar mazauna jihar Imo bisa dalilan tsaro.

An ruwaito wani jami'in gwamnatin jihar Imo, yana cewa babu ja- da- baya game da hakan.

Sai dai yayin da wasu 'yan arewacin Najeriyar ke ganin hakan wata wariya ce ake son nuna masu, wasu masana shari'a da masu fafutukar kare hakkin bil'adama duk sun bayyana katin da cewa ya saba ka'ida.

Bayanai dai sun nuna cewa an soma raba wannan katin shaida kyauta ga 'yan arewacin Nigeria mazauna Imo domin tabbatar da tsaro.