Dambarwa kan yunkurin tsige Nyako

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Ana jin gwamna Murtala Nyako ya shiga wannan gararin ne sakamakon adawar da ya ke yi da Shugaba Jonathan.

Ana ci gaba da dambarwa a jihar Adamawa ta Najeriya game da yunkurin tsige Gwamna Murtala Nyako da wasu 'yan majalisar dokokin jihar ke yi.

Majalisar dai ta sake zartar da wani kudiri da ya bai wa akawunta ikon sanar da Gwamnan da mataimakinsa sanarwar shirin tsige su ta kafafen yada labarai, bayan akawun ya kasa haduwa da su domin ya mika sanarwar hannu da hannu.

Sai dai Gwamnan a nasa bangaren, ya ce 'yan majalisar sun sabawa ka'ida da zartar da wannan kudurin, saboda wata kotu ta riga ta haramta musu yin hakan, don haka ba zai saurare su ba.

''Mu wannan abin ya zamar muna abin takaici, abin dariya; muna ganin ya zama kamar ba wasan yara ba ma ya zama hauka,'' inji Ahmed Sajoh, mai magana da yawun Gwamna Murtala Nyako.

Karin bayani