Ridda: An sake kama 'yar Sudan

Image caption Meriam ta haifi 'ya mace a kurkuku

Wasu majiyoyi a Sudan sun ce, an sake matar nan da aka yi wa hukuncin kisa saboda ridda, kwana daya bayan an sake ta.

Majiyoyin sun fada wa BBC cewa, wasu da ake zaton jami'an tsaro ne cikin farin kaya su 40 ne suka kama Meriam Ibrahim a filin jiragen sama na Khartum.

Meriam tare da mijinta Daniel Wan da 'ya'yansu na shirin fita daga Sudan ne yayin da aka kama su.

A ranar Litinin ne wata kotun daukaka kara a Sudan ta ba da umarnin a saki Meriam.

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba